<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>221</hymn_number>
<lyrics>[V1]
 1) Almasihu, pa babba, kai ne dutsen cetonmu.
 Sa mu cikin inuwarka, bar mu shiga kariyarka.
 Duk mun kasa adalci, duk mun aika zunubi,
 Kai madogararmu ne, kai dai matserarmu ne.

[V2]
 2) Ko mun kawo sadaka, ko mun daina ratsewa,
 Dukan namu ƙoƙari ba ya iya cetonmu.
 Kai kaɗai matsakanci, aikin sulhu naka ne.
 Mutuwarka da tashinka su sun kawo gafara.

[V3]
 3) Ga mu nan gun giciyenka, muna jiran ikonka.
 Kau da dukan zunubi, rashin ƙwazon Masu Bi.
 Da jini mai daraja, wanke mana zukata. Tsarkake mu duk yanzu don mu cika nufinka.

[V4]
 4) Ya maƃuyar tsarkaka, nuna ƙarfin cetonka.
 Ba mu ikon nasara, tsai da ikon magauta,
 Kwaƃi duk muguntarsu, rushe duk dabarbaru.
 Sai ka taya mu yanzu, ƙarfafa rayukanmu.</lyrics>
<title>Almasihu, Pa Babba, Kai Ne Dutsen Cetonmu LW221</title>
</song>